Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito cewa, muna rayuwa a wani zamani wanda, kamar yadda malamai da ƙwararru a fannin sadarwa suke bayyana shi, ya shahara da sunan zamanin mayar da ɗan’adam tamkar kayan kasuwanci. A cikin wannan yanayi, yayin tunawa da kwanakin makoki da shahada cikin zalunci ta Sayyida Fatima Zahra (AS), wadda ita ce shugabar matan talikai, tambayar da take gabanmu ita ce: Ta yaya za a yi amfani da sirar Sayyida Fatima (SA) mai cike da haske wajen sake dawo da ɗaukaka da mutuncin ɗan’adam a irin wannan zamani da yanayin zamantakewa?
Da farko, ya kamata a kula da cewa, a wannan zamani da kafafen sada zumunta da kafofin yaɗa labarai suka mamaye rayuwa, ana gina asalin mutuntaka da sanin kai bisa “tabbatarwa daga wajen mutum”. Wato, mutum yana ganin cewa sai an gan shi ne zai ji cewa yana da wani matsayi ko wanzuwa. Saboda haka, yana neman a yi masa alamar so (like) a kafafen sada zumunta, kuma a san shi ta hanyar wasu shahararrun samfuran kayayyaki (brands).
Wannan yana nufin cewa, abin takaici, asalin mutuntaka da sanin kai sun zama kamar wani abu da mutum yake aro daga wasu, maimakon ya samo su daga cikinsa.
Amma idan muka yi nazari mai zurfi kan muhimman ginshiƙan sirar Sayyida Fatima (SA), za mu fahimci cewa, asalin mutuntaka da sanin kai suna ginuwa ne bisa abin da mutum yake ƙunshe da shi da kuma ƙimomin da suke cikin zuciyarsa.
Idan mace ko yarinya a cikin al’umma ta fara neman darajarta a cikin taƙawa, ilimi da tasirin da take da shi a cikin al’umma, kamar rawar siyasa, al’adu da zamantakewa da Sayyida Fatima Zahra (AS) ta taka a lokacin da ya biyo bayan wafatin Manzon Allah (SAWA), to, babu shakka za ta fita daga zagayen neman tabbatar da darajarta ta hanyar nuna kanta ga mutane. A wannan yanayin ne za ta iya samar da yanayin da zai ba ta damar samun ɗaukaka da mutuncin ɗan’adam.
Bisa koyarwar addini tsarkakakkiya da aka samo daga koyarwar Ma’asumai (AS), mutuncin ɗan’adam yana tabbata ne idan tushen darajar mutum ya kasance shi kansa, ba hoton da yake nuna wa wasu mutane ba. Wannan shi ne ainihin kaiwa ga yarda da kai, wadda take samun cikakkiyar ma’ana ne a ƙarƙashin bautar Allah.
Idan muka yi nazari kan sirar Sayyida Fatima (SA), za mu fahimci cewa, ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙan salon rayuwarta shi ne abin da za a iya kira “sauƙin rayuwa mai ƙarfi da ɗaukaka.”
A haƙiƙa, sauƙin rayuwar da take yi bai samo asali daga rashin ƙarfi ko rashin iko ba ne, illa zaɓi ne da ta yi bisa sani da fahimta. Kamar yadda Sayyida Fatima (SA) ta nuna a aikace cewa, mutum zai iya kasancewa a matsayi mafi girma na gudanar da al’amuran zamantakewa da tasiri a cikin al’umma, a matsayin jagora mai zaburar da tunani da tarbiyya, ba tare da zama bawan kayan more rayuwa da yawan amfani da kayayyaki fiye da buƙata ba.
Saboda haka, ya kamata a ce, mutum yana komawa ga batun mutuncin ɗan’adam ne a lokacin da ya ɗaukaka kansa daga matsayin “mai amfani da kayayyaki kawai” zuwa matsayin “mai samar da ƙima da amfani ga al’umma.”
A wannan fanni, sirar Sayyida Fatima (SA) mai cike da haske tana koya wa mata da ’yan mata cewa, kowacce daga cikinsu tana iya zama sanadin kawo sauyi. Don haka, ya kamata ta ɗauki matakai domin samar da sauyin da ake buƙata, bisa kallon tauhidi da kuma ƙarƙashin tarbiyyar Ubangiji.
Wannan shi ne dalilin da ya sa a cikin sirar Ummu Abiha, wato Sayyida Fatima (SA), aka ba da muhimmanci na musamman ga batutuwan kunya da kiyaye mutunci, a matsayin wata irin garkuwar kariya.
A nan, kunya tana nufin iya sarrafa iyakokin mutum na kansa. Idan mace ko yarinya tana kiyaye iyakokinta na ciki da na zahiri bisa kunya, a haƙiƙa tana kare kanta ne daga fuskantar kallon wucewa kawai da kuma hukuncin da ake yankewa bisa fahimta ta sama-sama.
Ta wannan hanya, yayin da take tafiya a hanyar samun mutuncin ɗan’adam, za ta samu ni’imar kwanciyar hankali wadda take samuwa daga rashin buƙatar neman amincewa ko tabbatar da darajarta a wajen wasu a kowane lokaci.
A wata ma’anar, mutuncin ɗan’adam yana cikin ’yancin tunani da zuciya na mutum, domin idan mutum ya mayar da hankali wajen haɓaka ƙwarewarsa da abubuwan alherin da suke cikinsa, a fannoni daban-daban kamar ilimi da ɗabi’a, zai iya samun kwanciyar hankali. Wannan kwanciyar hankali kuma za ta taimaka masa wajen tafiya a hanyar samun rabauta a duniya da lahira.
Tabbas, a wannan fanni, kafofin yaɗa labarai masu riƙon amana a cikin al’ummar Musulunci ya kamata su yi amfani da koyarwa da salon rayuwar Sayyida Fatima (SA) wajen sauya ma’aunin da ake amfani da shi wajen tantance darajar mutum a tunanin masu sauraro da masu karatu.
Wannan yana nufin cewa, ta hanyar gabatar da hujjoji da bayanai masu gamsarwa, tare da yin amfani da fasahohin fasaha da ƙirƙira, ya kamata kafofin yaɗa labarai su sauya fahimtar mutunci daga abin da ya shafi zahiri zuwa ainihin ƙimar da take cikin mutum.
A lokaci guda, ya kamata a kula da cewa, ɗaya daga cikin manyan matsalolin da kafofin yaɗa labarai suke haifarwa shi ne ƙirƙirar saɓani tsakanin “kyawun ɗabi’a” da “kyawun zahiri.”
Saboda haka, kafofin yaɗa labarai masu riƙon amana bai kamata su sanya mace a matsayin wadda dole ne ta zaɓi ɗaya daga cikin waɗannan biyun ba. A maimakon haka, ya kamata su wuce wannan takaitaccen tunani, su zama masu bayyana da kuma yaɗa ma’anar “kyau mai cike da kamala da natsuwa” ko kuma “kyau mai hikima.”
Wannan yana nufin cewa, ya kamata su nuna cewa yin ado da kula da kai ba sa saɓani da kunya da mutuncin ɗan’adam, illa dai wani ɓangare ne na yadda mutum yake tafiyar da halayensa da kuma mutuntakarsa.
A wata ma’anar, kafofin yaɗa labarai ya kamata su bayyana cewa, mace za ta iya kiyaye ƙa’idojin kunya, tare da samun ƙarfin gwiwa da yarda da kanta, sannan ta taka rawar da ta dace da ita a fannonin al’adu da zamantakewa, ba tare da ta faɗa ƙarƙashin ra’ayoyin da suka shafi yawan amfani da kayayyaki da nuna kai ba.
Marubuci: Sayyid Muhammad Mahdi Musawi
Ra'ayinka